Iran Ta Kama wasu Fitattun ’Yan Siyasar ƙasar Bisa Zarginsu da Alaƙa da Amurka da Isra’ila.

Iran Ta Kama wasu Fitattun ’Yan Siyasar ƙasar Bisa Zarginsu da Alaƙa da Amurka da Isra’ila.

Hukumomin Iran sun kama mutane huɗu, ciki har da fitattun ’yan siyasar ƙasar masu ra’ayin sauyi su uku, bisa zargin ƙoƙarin tayar da hankalin siyasa da zamantakewa a ƙasar da kuma aiki don amfanin Amurka da Isra’ila a lokacin zanga-zangar adawa da gwamnati da ta auku a watan Janairu.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai Azar Mansouri da shugabar ƙungiyar Reform Front ta Iran; Mohsen Aminzadeh da wani tsohon jami’in diflomasiyya da Ebrahim Asgharzadeh, tsohon ɗan majalisar dokokin ƙasar. 
Har yanzu ba a bayyana sunan mutum na huɗun ba.

Bangaren shari’a na Iran ya bayyana cewa an kama mutanen ne bisa zargin shiryawa da jagorantar ayyukan da ke da nufin tayar da rikici a lokacin da ƙasar ke fuskantar barazanar tsaro daga ƙasashen waje. 
Hukumomin sun ce sun yi ƙoƙarin halatta ayyukan masu tayar da tarzoma a tituna.

Ƙungiyar Reform Front ta tabbatar da kamen a wata sanarwa, inda ta ce an kama Azar Mansouri daga gidanta bisa umarnin kotu ta hannun jami’an Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC). Sanarwar ta kuma ce an aika sammaci ga wasu manyan mambobin ƙungiyar.

Kamen ya zo ne a daidai lokacin da Iran ke fuskantar fushin jama’a sakamakon rikicin zanga-zangar watan Janairu, wadda ta samo asali daga matsin tattalin arziki kafin ta rikide zuwa gagarumin motsin adawa da gwamnati a faɗin ƙasar.

Gwamnatin Iran ta ce mutane 3,117 ne suka rasa rayukansu a lokacin rikicin, yayin da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama ke cewa adadin ya fi haka, ya yin da  kama dubban mutane a lokacin tarzomar.

Hukumomin Iran sun dora alhakin rikicin kan tsoma bakin ƙasashen waje, musamman Amurka da Isra’ila, zargin da ƙasashen biyu suka musanta.

Kamen fitattun ’yan siyasar ya ƙara tsananta yanayin siyasa a Iran, tare da janyo martani daga cikin gida da na ƙasashen waje, a yayin da ake ci gaba da tattaunawar diflomasiyya tsakanin Amurka da Iran akan shirinta na Nukiliya don rage tashin hankali a yankin.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: