Erling Haaland ya ci bugun fanareti a lokacin ƙarin lokaci, inda Manchester City ta samu nasara mai ban mamaki da ci 2–1 a kan Liverpool a filin wasa na Anfield a yau Lahadi, lamarin da ya rage tazarar da Arsenal ke da ita a saman teburin Premier League zuwa maki shida.
City na dab da shan kashi bayan da Dominik Szoboszlai ya zura kwallo mai ban sha’awa ta bugun tazara domin bai wa Liverpool ragaman wasan.
Sai dai cikin mintuna shida kacal kafin a tashi wasan, Bernardo Silva ya rama kwallon, abin da ya tayar da wasan zuwa wani sabon salo.
Haaland daga bisani ya nuna kwarewa da natsuwa inda ya ci bugun fanareti bayan mai tsaron ragar Liverpool, Alisson Becker, ya yi wa Matheus Nunes keta a cikin akwatin fanareti.
A cikin wannan yanayi ne, aka soke wata kwallo da City ta ci bayan duba ta a na'uran VAR, yayin da Szoboszlai ya samu jan kati a lokacin.
Nasarar ita ce ta farko da Manchester City ta samu a Anfield akan Liverpool a gaban magoya bayanta tun shekarar 2003, kuma hakan ya sake matsa lamba kan Arsenal da ke neman lashe kofin Premier na farko cikin shekaru 22.
A bangaren Liverpool kuwa, shan kashin, ya sake jefa shakku kan burinsu na samun gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta Champions League a kakar wasa mai zuwa. Yanzu haka suna matsayi na shida a teburin gasar, maki hudu a bayan kungiyoyi 5 da ke sahun gaba.
Kungiyoyin biyu sun raba lashe kofin Premier League sau takwas a jere a shekarun baya, amma duk da haka sun nuna rauni a wannan kakar, abin da ya bai wa Arsenal damar yin nisa a saman teburin gasar.
Manchester City ta mamaye wasan a rabin farko amma ta kasa amfani da damar da ta samu.
Haaland, wanda ya ci kwallo guda daya kacal daga budadden wasa a wasanninsa 13 na baya-bayan nan, ya rasa damarmaki da dama, inda Alisson ya hana shi zura kwallo a yinkuri da yayi da dama.
Liverpool ta farfado bayan hutun rabin lokaci, inda Szoboszlai ya sake nuna bajintarsa da bugun tazara mai kyau wanda ya buge gefen sandar raga kafin ya shiga kwallo, sai dai daga baya City ta juya wasan a mintunan ƙarshe domin kwashe maki uku masu muhimmanci.
_3.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment