Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya shafi tirela wacce ke kan hanyar zuwa Gujungu a Jihar Jigawa, wanda ya faru a Kwanar Barde, Karamar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano.
Hatsarin, wanda ya auku da safiyar Lahadi, an ce ya faru ne sakamakon tukin ganganci, lamarin da ya jikkata wasu da dama da ke kwance suna karɓar magani a asibitoci daban-daban.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, ya bayyana alhininsa kan lamarin, yana mai cewa hatsarin abin tausayi ne kuma babban rashi ne ga iyalan da abin ya shafa da al’ummar jihar baki ɗaya.
Martanin gwamnan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Daraktan yada Labarai da Hulɗa da Jama’a na Fadar Gwamnatin Kano, Sunusi Dawakin-Tofa, ya fitar a yau Lahadi.
A cewar sanarwar, tirelar na kan hanyarta zuwa Gujungu ne lokacin da ta yi hatsari, wanda ake zargin tukin ganganci ne ya haddasa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 30 tare da jikkata wasu da dama.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah Ya jikansu, Ya kuma bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi. Haka kuma, ya roƙi Allah Ya ba wa waɗanda ke karɓar magani cikin saurin samun lafiya.
Gwamnan ya umarci Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano da ta tabbatar an bai wa dukkan waɗanda hatsarin ya shafa da ke asibitoci kulawa ta kyauta da ingantacciyar lafiya ba tare da ɓata lokaci ba.
Haka kuma, ya umurci Ofishin Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Jinƙai da ya gaggauta tantance halin da ake ciki tare da ɗaukar matakan tallafa wa iyalan waɗanda suka rasu.
Gwamna Yusuf ya kuma gargaɗi direbobi, musamman masu tukin manyan motoci, da su guji tukin ganganci tare da bin dokokin zirga-zirga domin kauce wa faruwar irin wannan masifa a nan gaba.

0 Comments:
Post a Comment