Gwamnatin Jihar Kogi ta bayar da umarnin rufe wasu kasuwanni da tashoshin mota na wucin gadi a yankin yammacin jihar domin tallafawa ayyukan tsaro da ake ci gaba da gudanarwa.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na jihar, Mista Kingsley Femi Fanwo, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Lokoja yayin ganawa da manema labarai.
Ya ce matakin na da nufin fatattakar ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka da ke aiki a wasu sassan jihar.
Fanwo ya bayyana cewa rufe kasuwannin da tashoshin motocin zai hana isar da kayan abinci da sauran kayayyakin tallafi ga masu aikata laifuka da kuma masu ba su bayanai.
A cewarsa, umarnin ya shafi wasu al’ummomi a kananan hukumomi bakwai da suka hada da Lokoja, Kogi, Kabba/Bunu, Ijumu, Mopa Muro, Yagba West da Yagba East.
Ya kara da cewa matakin na wucin gadi ne kawai, kuma za a janye shi nan take bayan kammala ayyukan tsaro cikin nasara.
Ya kuma tunatar da cewa a ranar 4 ga Fabrairu, 2026, gwamnatin jihar ta rufe dukkan makarantun firamare da sakandare a jihar domin kare rayuka da dukiyoyi sakamakon kalubalen tsaro da ake fuskanta.
_1.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment