NLC ta yi barazanar gudanar da zanga-zanga kan gyaran Dokar Zaɓe

NLC ta yi barazanar gudanar da zanga-zanga kan gyaran Dokar Zaɓe

Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta yi gargaɗin yiwuwar gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da kuma kauracewa zaɓe, bisa abin da ta kira ruɗani da saɓanin ra’ayoyi daga Majalisar Dattawa kan gyaran Dokar Zaɓe, musamman game da tura sakamakon zaɓe ta hanyar na'ura.

NLC ta zargi Majalisar Dattawa da raunana amincewar jama’a ga tsarin zaɓen Najeriya, sakamakon rashin bayyana a sarari ko tura sakamakon zaɓe ta lantarki zai zama wajibi.

A cikin wata sanarwa da Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce: “Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa na nuna matuƙar damuwa kan ruɗani da kuma labarai masu karo da juna da ke fitowa daga Majalisar Dattawa dangane da gyaran Dokar Zaɓe ta 2022, musamman game da tura sakamakon zaɓe ta na'ura.”

A cewar NLC, rashin fayyace matsayar Majalisar Dattawa na barazana ga sahihancin zaɓe da amincewar jama’a, tana mai jaddada cewa “’yan Najeriya sun cancanci tsarin da ke da gaskiya, inda ba kawai ana ƙirga ƙuri’u ba, har ma ana ganin yadda ake ƙirga su.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, bayanan da ke fili sun nuna cewa an ƙi amincewa da gyaran da zai tilasta wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) tura sakamakon zaɓe ta na'ura kai tsaye a lokaci guda, inda aka bar tsarin da ke bai wa INEC ‘yancin zaɓi kamar yadda yake a baya.

“Wannan ya haifar da fargaba a faɗin ƙasa, kuma bayanan da aka yi daga baya sun ƙara jefa al’amari cikin ruɗani,” in ji ƙungiyar.

NLC ta yi gargaɗin cewa “ruɗanin doka” a wannan muhimmin lokaci bayan zaɓukan gama-gari na 2023 na iya saka shakku a cikin tsarin zaɓen ƙasa.

Ƙungiyar ta buƙaci Majalisar Dattawa da ta fitar da “gaggawa,  kuma a bayyane” kan ainihin tanade-tanaden da aka amince da su, ciki har da kalmomin ƙarshe da dalilan yanke shawarar.

Sanarwar ta ce: “Dole ne shugabancin Majalisar Dokoki ya tabbatar da cewa tsarin daidaitawa ya samar da dokar ƙarshe mai cikakken bayani; duk wani ruɗani kan turawa da tattara sakamakon zaɓe cin mutunci ne ga dimokuraɗiyyarmu.”

NLC ta jaddada cewa gyarar Dokar Zaɓe dole ne ya tanadi umarni kai tsaye da zai tilasta wa INEC turawa da tattara sakamakon zaɓe ta na'ura daga rumfunan zaɓe a lokaci guda, tana mai gargaɗin cewa rashin yin hakan na iya haifar da matakan ƙalubale masu tsanani.

“Rashin saka tura sakamakon zaɓe ta na'ura a lokaci guda zai kai ga ɗaukar matakan zanga-zanga kafin lokacin da bayan zaɓe, ko kuma kauracewa zaɓen gaba ɗaya,” in ji ƙungiyar.

“'Yan Nigeriya, ma’aikata da ’yan ƙasa na sa ido. 
Ƙasarmu dole ta zaɓi hanyar tsabta da gaskiya. Dole ne mu guji irin ruɗanin da ya biyo bayan sabbin Dokokin Haraji. 
Lokacin dokoki masu gaskiya da fifita jama’a ya yi.”

Gargaɗin na zuwa ne bayan Majalisar Dattawa ta amince da kudirin gyaran Dokar Zaɓe ta 2022 (Soke da Sake Zartarwa) ta shekarar 2026, bayan karatu na uku a ranar 4 ga Fabrairu, 2026.

A yayin amincewa da kudirin, Majalisar Dattawa ta ƙi sashe na 60(3), wanda zai tilasta wa shugabannin rumfunan zaɓe tura sakamakon ƙuri’u ta na'ura kai tsaye zuwa dandalin kallon sakamakon INEC a lokaci guda. Wannan sashe na da nufin sanya tsarin ya zama wajibi.

An maye gurbinsa da tsarin da ke bai wa hukuma ’yancin zaɓi na “tura” sakamakon bayan an ƙirga ƙuri’u kuma an bayyana su a fili a rumfunan zaɓe.

Ƙungiyoyin farar hula da ’yan adawa sun soki matakin Majalisar Dattawa, suna kallonsa a matsayin koma-baya ga ci gaban dimokuraɗiyyar Najeriya.

Sai dai Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya kare matakin majalisar, yana mai cewa ba a ƙi tura sakamakon zaɓe ta na'ura ba, kuma ya yi alƙawarin cewa ba za a tsorata majalisar ba.

A halin da ake ciki, Majalisar Dattawa ta sanya ranar Talata, 10 ga Fabrairu, 2026, domin zaman gaggawa. Ana sa ran zaman zai iya duba yiwuwar sake nazarin sashe da aka ƙi, sakamakon matsin lambar jama’a da kuma yiwuwar ƙalubalen shari’a daga wasu lauyoyi ciki har da Femi Falana, lamarin da ka iya yin tasiri ga makomar dimokuraɗiyyar Najeriya da tsarin tabbatar da sahihancin zaɓe.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: