Kungiyar IPOB Ta Soke Umarnin Zama a Gida Bisa Umarnin Jagoranta Nnamdi Kanu.


Kungiyar dake fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) ta sanar da soke umarnin zama a gida a dukkan jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Kungiyar ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar, inda ta ce matakin ya biyo bayan umarni daga jagoranta da ke tsare ne, Nnamdi Kanu.

A cewar IPOB, Kanu ya umarci shugabannin kungiyar da su dakatar da matakin zama a gida domin tabbatar da zaman lafiya da kuma dawo da harkokin tattalin arziki da zamantakewa yadda ya kamata a yankin.

Kungiyar ta ce an dauki wannan mataki ne domin rage wahalhalun da mazauna yankin ke fuskanta, musamman ‘yan kasuwa, ma’aikata, dalibai da sauran jama’a, sakamakon tsaikon da umarnin ya haddasa.

IPOB ta bukaci al’ummar Kudu maso Gabas da su ci gaba da gudanar da halaltattun ayyukansu ba tare da tsoro ba, tare da jaddada kudirinta na bin hanyoyin lumana.

Har ila yau, kungiyar ta sake jaddada aniyarta na kin amfani da tashin hankali, tana mai cewa tana da niyyar ci gaba da fafutuka ta hanyar zaman lafiya.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: