Ƙasar Saudiyya ta sake jaddada goyon bayanta ga cikakken ikon ƙasar Sudan da mutuncin yankunanta, tare da yin Allah-wadai da abin da ta kira “hare-haren ta’addanci” da dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka kai a jihohin arewa da kudancin Kordofan, inda aka kashe mutane da dama, ciki har da mata da ƙananan yara.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta fitar a ranar Asabar, ƙasar ta yi kakkausar suka kan “tsoma bakin ƙasashen waje” a harkokin Sudan, tana zargin wasu ɓangarori da ba a bayyana sunayensu ba da ci gaba da shigo da makamai ba bisa ƙa’ida ba, da mayaƙan haya da kuma ’yan ƙasashen waje, lamarin da ke ƙara tsawaita yaƙin da ya shafe kusan shekaru uku yana gudana.
Sanarwar ta zo ne bayan Sudan Doctors Network, wata ƙungiyar jin ƙai, ta bayyana cewa wani harin jirgin yaƙi mara matuƙi (drone) da RSF ta kai kan wata mota da ke ɗauke da iyalan ’yan gudun hijira a arewacin Kordofan ya kashe aƙalla mutane 24, ciki har da yara takwas. Harin na daga cikin jerin hare-haren drone da aka kai kan ayarin motocin tallafin jin ƙai da na dakon man fetur a yankin. A ranar Juma’a kuma, an kai hari kan ayarin motocin Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP), inda aka kashe aƙalla mutum ɗaya.
Faɗa tsakanin RSF da rundunar sojin Sudan ya ƙara ƙamari a yankin Kordofan a watannin baya, musamman bayan faɗuwar birnin el-Fasher hannun RSF a watan Oktoba.
Rikicin da ya shafe kusan shekaru uku yana gudana ya kashe kimanin mutane 40,000, tare da jefa sama da mutane miliyan 21 — kusan rabin al’ummar Sudan — cikin matsanancin ƙarancin abinci.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta ce hare-haren RSF “ba su da wata hujja kwata-kwata” kuma “suna karya dukkan ƙa’idojin jin ƙai da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa.”
Ta buƙaci RSF da ta dakatar da hare-haren nan take, ta kuma mutunta dokokin jin ƙai na duniya tare da bin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a Jeddah a shekarar 2023, domin tabbatar da isar da agaji ga masu buƙata.
Haka kuma, sanarwar ta yi nuni da cewa wasu ɓangarori na waje na ci gaba da hura wutar rikicin ta hanyar aika makamai da mayaƙa, duk da ikirarin cewa suna goyon bayan warware rikicin ta hanyar siyasa.
Wannan sanarwa ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Sudan ke zargin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da tallafa wa RSF da makamai da kuɗi.
A bara, Sudan ta shigar da ƙara a gaban Kotun Duniya (ICJ), tana zargin UAE da hannu a kisan kare dangi da RSF ta aikata kan al’ummar Masalit a jihar Yammacin Darfur, sai dai UAE ta musanta waɗannan zarge-zarge.
A wani lamari na daban, Saudiyya ta kuma zargi UAE da goyon bayan ƙungiyar Southern Transitional Council (STC) mai neman ballewa a Yemen.
Ƙungiyar STC, wadda da farko ke cikin gwamnatin Yemen da Saudiyya ke marawa baya, ta ƙaddamar da gagarumin farmaki a watan Disamban da ya gabata a jihohin Hadramout da al-Mahra, da nufin kafa ƙasa mai zaman kanta. Wannan ya haddasa rabuwar kai a cikin gwamnatin Yemen da ake marawa baya a duniya, tare da jawo hare-haren sama daga Saudiyya kan STC.
Daga bisani UAE ta janye dakarunta daga Yemen, tana mai cewa tana goyon bayan tsaron Saudiyya.
Duk da haka, Saudiyya da UAE duka sun kasance mambobin ƙungiyar sojin Larabawa da aka kafa a shekarar 2015 domin fuskantar ’yan Houthi, waɗanda suka ƙwace cikakken iko da birnin Sanaa, fadar mulkin Yemen.
_2.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment