Shugaba Tinubu Zai Kai Ziyarar aiki Birtaniya Bisa Gayyatar Sarki Charles III.

Shugaba Tinubu Zai Kai Ziyarar aiki Birtaniya Bisa Gayyatar Sarki Charles III.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu zuwa Ƙasar Birtaniya daga ranar 18 zuwa 19 ga Maris, 2026, bisa gayyatarsa a hukumance daga Sarki Charles na Uku.

Sanarwar ziyarar ta fito ne a ranar Lahadi ta shafin X (tsohon Twitter) na fadar sarautar Birtaniya, inda aka bayyana cewa Sarki Charles III da Sarauniya Camilla za su karɓi Shugaba Tinubu a fadar Windsor Castle. 
Shugaban zai kasance tare da matarsa kuma Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu.

A cewar sanarwar, “Shugaban Tarayyar Najeriya, Mista Bola Ahmed Tinubu, tare da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Misis Oluremi Tinubu, ya amince da gayyatar Mai Martaba Sarki domin kai ziyarar aiki zuwa Ƙasar Birtaniya daga Laraba, 18 ga Maris, zuwa Alhamis, 19 ga Maris, 2026. 
Sarki da Sarauniya za su karɓi ziyarar a fadar Windsor Castle.”

Da yake mayar da martani kan sanarwar, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana ziyarar a matsayin tarihi, inda ya ce ita ce ziyarar aiki ta farko da wani shugaban Najeriya zai kai Birtaniya cikin shekaru 37.

Ya ce, “An tabbatar da ziyarar aiki ta farko da wani shugaban Najeriya zai kai Birtaniya cikin shekaru 37. Shugaba Tinubu da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu, za su kasance baƙi a wurin Sarki Charles da Sarauniya Camilla daga 18 zuwa 19 ga Maris, 2026.”

Ziyarar ƙarshe da wani shugaban Najeriya ya kai Birtaniya ta kasance a shekarar 1989, lokacin da tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, marigayiya Sarauniya Elizabeth ta Biyu ta karɓe shi na tsawon kwanaki huɗu.

Kamfanin sadarwa na BBC ya bayyana ziyarar aikin a matsayin wata hanya ta diflomasiyya wadda ke haɗa al’adun sarauta da karɓar baƙi domin ƙarfafa alaƙa da ƙasashen abokan juna.

Shugaba Tinubu da Sarki Charles III, waɗanda duka suka hau mulki a watan Mayun 2023, sun haɗu sau da dama. 
A watan Nuwamban 2023, Shugaba Tinubu ya gana da Sarkin a Dubai gabanin taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi (COP28), inda ya bayyana ganawar a matsayin muhimmiyar hanya ta zurfafa alaƙar ƙasashen biyu. Haka kuma, a watan Satumban 2024, Sarki Charles ya karɓi Shugaba Tinubu a fadar Buckingham Palace a wata ganawa ta musamman.

Sarki Charles III na da tsohuwar alaƙa da Najeriya, kuma ya taɓa bayyana sha’awarsa ga harshen Pidgin da kuma wakokin Afrobeats. Kafin hawansa karagar sarauta, ya kai ziyara Najeriya sau huɗu a matsayin Yariman Wales a shekarun 1990, 1999, 2006 da 2018. A ziyarar 2018, Sarauniya Camilla, wadda a wancan lokaci take Duchess of Cornwall, ta kasance tare da shi.

A shekarar 2023, Cibiyar King’s Trust International, wadda a da ake kira Prince’s Trust, ta fara ayyuka a Najeriya, inda ta ƙaddamar da shirye-shirye da nufin rage rashin aikin yi a tsakanin matasa.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: