Dan Majalisar Amurka Riley Moore Ya Yi Gargadi Kan Tasirin Taimakon Ƴan Aware a Najeriya.

Dan Majalisar Amurka Riley Moore Ya Yi Gargadi Kan Tasirin Taimakon Ƴan Aware a Najeriya.

Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yi gargadin cewa duk wani yunƙuri na tallafawa ƴan aware masu neman ɓallewa daga Najeriya ko raba kan al'umma zai ƙara ta'azzara rashin tsaro ne, tare da sanya Kiristoci cikin haɗari a faɗin ƙasar, har ma a wasu sassan Afirka.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, Moore ya bayyana cewa ya gudanar da ziyarar bincike a Najeriya domin fahimtar yanayin zargin da ake yi na cin zarafin Kiristoci.

Moore ya ce a ƙarƙashin wannan ziyara, ya tattauna da jami’an gwamnati, shugabannin coci-coci, ƙungiyoyin agaji, da kuma mutanen da rikice-rikice ya raba da gidajensu, domin samun cikakken fahimtar kalubalen da Kiristoci ke fuskanta, musamman a Arewa.

“Na yi tattaki zuwa Najeriya kuma na yi tarurruka da dama da jami’an Najeriya, shugabannin coci-coci, ƙungiyoyin agaji a fadin ƙasar, da 'yan gudun hijira, domin samun fahimtar yadda ake cin zarafin Kiristoci a Najeriya,” in ji Moore.

Dan majalisar ya ƙara da cewa, a binciken da ya gudanar, batun nuna banbanci bai fito fili ba, amma duk wani ƙoƙarin ƙarfafa gwiwar ƴan aware zai cutar da Kiristoci ne a Najeriya, musamman a Arewancin ƙasar.

Moore ya yi gargadin cewa duk wani yunƙurin wargaza zaman lafiya a Najeriya zai iya ƙara wa ƴan ta'adda ƙarfi tare da jefa Kiristoci cikin hatsari.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: