Gwamnatin Tarayya ta amince da sake buɗe iyakar ƙasa ta Tsamiya da ke Jihar Kebbi zuwa Jamhuriyar Benin, domin bunƙasa harkokin kasuwanci na ƙetare da rage matsin tattalin arziƙin da aka samu sakamakon rufe iyakar na dogon lokaci.
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba da wannan mataki, inda ya bayyana shi a matsayin ci gaba mai kyau ga jihar da ma tattalin arziƙin ƙasa baki ɗaya.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar a shirye take ta yi aiki tare da Hukumar Kwastam ta Najeriya da sauran hukumomin tsaro, domin tabbatar da cewa buɗe iyakar ba zai kawo barazana ga tsaron ƙasa ba.
Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi, ne ya sanar da amincewar a ranar Asabar, inda ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya ba da umarnin sake buɗe iyakar bayan shawarwari da masu ruwa da tsaki.
Adeniyi ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da masu fitar da kaya da ‘yan sufuri da ‘yan kasuwar albasa a Jihar Kebbi.
Ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta yi watsi da ƙalubalen da masu kasuwanci da al’ummomin iyaka ke fuskanta sakamakon rufe iyakar ba. Ya jaddada cewa za a buɗe iyakar ne bisa tsauraran ƙa’idojin tsaro, domin hana masu aikata laifuka yin amfani da hanyoyin kasuwanci ba bisa ka’ida ba.
“Ba mu yi shiru kan halin da ake ciki ba. A bayan fage, duk masu ruwa da tsaki suna aiki dare da rana domin shawo kan waɗannan matsaloli,” in ji Adeniyi. “Dole ne mu sauƙaƙa kasuwanci ba tare da yin sakaci da tsaron ƙasa ba.”
Babban jami’in Kwastam ɗin ya bayyana cewa kwanan nan Najeriya ta karɓi wata tawaga ta gaggawa daga Hukumar Kwastam ta Jamhuriyar Nijar da Ƙungiyar Kasuwancinta a Abuja, domin hanzarta warware matsalar cunkoson kasuwanci.
Ya ƙara da cewa Hukumar Kwastam za ta yi amfani da tsarin fasahar sadarwa (ICT) da zai haɗa hukumomin kwastam na Benin da Nijar, domin tabbatar da sahihancin bayanai, sa ido da kuma sauƙaƙa ayyukan fitar da kaya.
Adeniyi ya kuma gargaɗi masu safarar kaya da su guji karkatar da kaya daga hanyoyin da aka amince da su, yana mai cewa duk motar kaya da aka samu a wajen hanyar da aka kayyade za a ƙwace ta.
Ya ce an riga an gurfanar da wasu masu laifi tare da dakatar da jami’an da suka karya doka, kuma Hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa wajen ɗaukar matakin shari’a kan duk wanda ya karya doka ba.
Ya kuma jaddada muhimmancin bunƙasa al’ummomin iyaka, yana mai cewa cigaban da ya haɗa kowa zai ƙara tsaro da haɗin kai a yankunan iyaka.
A nasa jawabin, Gwamna Nasir Idris ya bayyana sake buɗe iyakar a matsayin abin farin ciki, inda ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta tallafa wa ayyukan Hukumar Kwastam da sauran jami’an tsaro. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta tallafa wa iyalan jami’an Kwastam da aka kashe a bakin aiki, bisa tsarin da gwamnati ta tanada.
Haka kuma, ya ce gwamnatin jihar za ta ba da motoci kirar Hilux guda biyu domin taimaka wa ayyukan buɗe iyakar Tsamiya.
A wajen taron, wani babban jami’i daga Hukumar Kwastam ta Jamhuriyar Benin, Immora Idrisu, ya yaba wa Najeriya bisa wannan mataki, tare da tabbatar da aniyar ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen biyu.
Ya ce Hukumar Kwastam ta Benin za ta ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da Kwastam ta Najeriya domin tabbatar da ingantaccen kasuwanci mai tsaro.
Tun da farko, Shugaban Ƙungiyar Manoman Albasa, Masu Sarrafawa da ‘Yan Kasuwa ta Najeriya, Isa Aliyu, ya ce hanyar Tsamiya tana da matuƙar muhimmanci ga rayuwar manoman albasa da ‘yan kasuwanta.
Ya bayyana cewa albasa kaya ce mai saurin lalacewa, inda kowace awa ta jinkiri ke janyo asara.
Ya ƙara da cewa rufe iyaka na tilasta kasuwanci shiga haramtattun hanyoyi, yana rage sa ido da kuma kudaden shiga na gwamnati.
A cewarsa, sake buɗe iyakar zai taimaka wajen cimma manufar Shugaba Tinubu ta bunƙasa tattalin arziki da haɓaka kudaden shiga na cikin gida ga jihohin da ke noma albasa da samar da ayyukan yi da kuma inganta tattara bayanan kasuwanci.

0 Comments:
Post a Comment