Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Amurka kan batun nukiliya, muddin tattaunawar ba ta ƙunshi matsin lamba ko barazana ba.
Araqchi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kafar watsa labarai ta Al Jazeera, kwana guda bayan Iran da Amurka sun amince su ci gaba da tattaunawa bayan yadda ɓangarorin biyu suka nuna gamsuwa da zagayen farko da aka gudanar a ƙasar Oman.
Araqchi bai bayyana takamaiman lokacin da za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar ba.
Sai dai shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ana sa ran za a sake ganawar a farkon mako mai zuwa.
Shugaban Amurka ya sha yin barazanar kai hari kan Iran, musamman bayan Washington ta ƙara girke jiragen ruwan yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Amurka na matsa lamba kan Tehran da ta dakatar da bunƙasa sinadarin Uranium, wanda ke iya share hanya zuwa kera makaman nukiliya da kuma makamai masu cin dogon zango.
Sai dai Iran ta nanata cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne kaɗai.
Ministan harkokin wajen Iran ya ce ƙasarsa za ta tattauna da Amurka ne kawai kan batun nukiliya, kuma ba za ta amince da faɗaɗa tattaunawar zuwa wasu batutuwa ba.
Ya jaddada cewa Tehran na maraba da tattaunawa bisa mutunta juna, amma ba za ta shiga tattaunawa ƙarƙashin matsin lamba ko barazana ba.
A watan Yunin shekarar da ta gabata ne Amurka ta kai hari kan wani wuri da take zargin Iran na bunƙasa sinadarin Uranium a cikinsa.
Daga baya Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan wani sansanin sojin Amurka da ke Qatar.
Araqchi ya yi gargaɗin cewa Iran za ta ɗauki irin wannan mataki idan aka sake kai mata hari.
Ya ƙara da cewa Iran ba ta da niyyar kai hari kai tsaye kan Amurka, amma za ta kai farmaki kan sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya idan an kai mata hari.
Ya kuma jaddada cewa Iran ba za ta kai farmaki kan ƙasashen makwabta ba, illa sansanonin sojin Amurka da ke yankin.

0 Comments:
Post a Comment