Dan wasan gaba na Kungiyar kwallon kafar Chelsea, Cole Palmer ya kafa tarihi a gasar Premier League bayan ya zama dan wasa na farko da ya zura kwallo uku a farkon rabin Lokaci karo na uku a gasar Premier League.
Palmer ya samu nasaran ne a wasan da Chelsea ta yi nasara a kan Wolverhampton Wanderers da ci 3-1 a Molineux, inda ya zura kwallaye uku a raga kafin a tafi hutun rabin lokaci a ranar Asabar.
Dan wasan na Ingila a baya ya yi irin wannan fajintar a farkon rabin lokaci a wasannin da Chelsea ta doke Everton da Brighton & Hove Albion, abin da ya sa ya zama dan wasa daya tilo a tarihin gasar Premier da ya yi irin wannan nasarar sau uku.

0 Comments:
Post a Comment