Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya mika sakon ta’aziyyar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ga gwamnati da al’ummar jihar Kwara

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya mika sakon ta’aziyyar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya mika sakon ta’aziyyar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ga gwamnati da al’ummar jihar Kwara sakamakon hare-haren kisan gilla da aka kai a kauyukan Woro da Nuku a karamar hukumar Kaiama.

Hare-haren, wadanda rahotanni suka ce 'yan kungiyar Islama ta Lakurawa ne suka kai a ranar 3 ga watan Fabrairu, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da lalata dukiyoyi.

Shettima, wanda ya yi magana a madadin shugaba Tinubu a wata ziyarar jaje da ya kai jihar Kwara a ranar Asabar, ya bayyana kashe-kashen a matsayin “cin zarafin da ba za a amince da shi ba na ’yancin mutane na gudanar da addininsu cikin lumana” ya kuma ce girman kashe-kashen “ya firgita ‘yan Najeriya.”

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kwara, Rafiu Ajakaye ya fitar, Shettima ya yi wa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq jawabi a gidan Ahmadu Bello dake Ilorin, inda ya ce wadanda abin ya shafa sun kasance masu son zaman lumana ne na al’ummomin da suka sadaukar da rayuwarsu wajen gina rayuwarsu tare da gudanar da addininsu bisa tsarin da addinin Musulunci ya umarce su.

Ya kara da cewa, garin "Kaima da Baruten, har ma da yankin Batonu na tsohuwar Borgu… an san su da aiwatar da tsarin Musulunci mafi kyawu tsawon ƙarni har sai da wani baƙon addini… ya mamaye waɗannan al'ummomin."

Shetima ya ba da tabbacin cewa an tura wata bataliyar sojojin Najeriya domin kawar da barazanar da ake yi a Kaiama da kewaye, yana mai jaddada cewa “dukkanin hannu na nan a kan tabbatar da cewa an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a wadannan al’ummomin.”

Ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma saka musu da Al-Jannah Firdaus, ya kuma roki gafara ga iyalai da jama’ar garin Kaiama.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: