Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga ‘yan kasuwar singa da iftila'in gobara ta shafa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga ‘yan kasuwar singa da gobara ta shafa Kano, a wani mataki na rage musu asarar da suka yi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar jajantawa da ya kai kasuwar, a ranar Alhamis.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban daraktan yada labarai labarai na fadar gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Gwamna Yusuf ya nuna damuwarsa kan irin asarar da ‘yan kasuwar ke yi, ya kuma ba su tabbacin gwamnatin jihar na kokarin kyautata rayuwarsu da samun sauki cikin gaggawa.
“Na yi matukar bakin ciki da abin da ya faru a nan, gwamnati ba za ta yi watsi da ku a cikin wannan mawuyacin lokaci ba,” inji gwamnan a lokacin da yake jawabi a kasuwar.
Gwamnan ya samu tarba daga Shugaban Kasuwar Singa, Barista Junaidu Muhammad Zakari da dattijon kasuwar Alhaji Sabi’u Bako da kuma mai filin da abin ya shafa Alhaji Munzali Mazaf.
Baya ga kunshin tallafin, Gwamna Yusuf ya ba da umarnin fadadawa tare da gyara hanyoyin cikin kasuwar nan take domin saukaka zirga-zirga da bunkasa harkokin kasuwanci.
Ya kuma amince da bayar da kyautar Naira biliyan 3 na ayyukan fadada hanyoyin mota da gyaran hanyoyin da suka shafi titin Bello da titin Ado Bayero da Kandoki da Yolawa da kuma titin Kwangiri da nufin rage ambaliyar ruwa da cunkoson ababen hawa a sassan manyan kasuwannin Kano.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin farfado da Kasuwar ta Singa, inda ya jaddada kudirin gwamnatinsa na sabunta kasuwanni a fadin jihar a wani bangare na shirin sabunta birane da bunkasa tattalin arziki.
Ya umurci ’yan kwangilar da ke gudanar da ayyukan hanyoyin da su hada kai su fara aiki cikin kwanaki 10.
Shugabanni da dattawan kasuwar sun nuna jin dadinsu ga gwamnan bisa ziyarar da ya kai musu, inda suka bayyana matakin a matsayin wanda ya dace da kuma tausayi.
Sun kuma yabawa gwamnatin jihar bisa jajircewarta na inganta ababen more rayuwa da tallafawa ‘yan kasuwa a manyan cibiyoyin kasuwanci na Kano.

0 Comments:
Post a Comment