Manchester United ta samu nasaran doke Tottenham da ci 2-0 a wasan Premier League mako na 25

Manchester United ta samu nasaran doke Tottenham da ci 2-0 a wasan Premier League mako na 25.

Kungiyar kwallon kafar Manchester United ta samu nasaran doke Tottenham da ci 2-0 a wasan Premier League mako na 25, inda Bryan Mbeumo da Fernendes su ka zura kwallaye biyun da yaba Sabon Kociyan rikon kwaryar Manchester United nasara a dukkanin wasanni hudun da ya Jagoranci Kungiyar tun bayan sallamar Ruben Amorin da Kungiyar ta yi a farkon watan junairu.

Dan wasan Manchester Bryan Mbeumo ne ya fara zura kwallon farko a minti na 38, jim kadan bayan an sallami C. Romero saboda keta da yayi dan wasan United, Casemiro.
Bayan an dawo hutun rabin Lokaci ne Bruno Fernandes ya zura ta biyu a minti na 80.

Nasaran ya sake ba United daman cigaba da zama a mataki na 4 a teburin da maki 44 Inda take bayan Aston Villa wacce ke mataki na 3 da maki 46 Kafin ta kece raini tsakaninta da AFC Bournemouth.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: