Dubban mutane ne suka halarci Jana'izar mutum 32 da suka rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai a Masallaci a ƙasar Pakistan.

Dubban mutane ne suka halarci Jana'izar mutum 32 da suka rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai a Masallaci a ƙasar Pakistan.

Dubban mutane ne suka halarci Jana'izar mutum 32 da suka rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai a Masallaci a ƙasar Pakistan.

Dubban jama'a a Pakistan sun hallara a babban birnin ƙasar, Islamabad domin jana'izar wadanda harin kunar bakin wake ya hallaka a wani masallacin 'yan Shi'a da ke birnin a lokacin sallar Juma'a, harin da ya kashe mutane akalla 32 tare da jikkata wasu mutum 170.

kungiyar ISIL (ISIS) mai dauke da makamai ce ta dauki alhakin kai harin bam din na ranar Juma'a wanda ya afku a masallacin Khadija Tul Kubra da ke yankin Tarlai Kalan a wajen birnin Islamabad.

Harin dai shi ne mafi muni da aka kai a birnin na Islamabad tun wanda a taba kaiwa a watan Satumban 2008, lokacin da wata babbar mota dauke da bam ta kashe mutane fiye da 60 tare da lalata wani bangare na otal din Marriott. 
Yayin da ba kasafai ake samun tashin bama-bamai a babban birnin kasar da ke da tsaro ba, wannan shi ne karo na biyu da aka kai irin wannan hari cikin watanni uku, lamarin da ke kara nuna fargabar komawar tashe-tashen hankula a manyan biranen Pakistan.

Wakilin kafar talabijin na Al Jazeera, Kamal Hyder, wanda yake bayar da rahoto daga Islamabad, ya ce mutanen da ya zanta da su sun yi imanin cewa ana kai hare-haren ne akan fararen hula.

"Sun ce wannan koma baya ne na tsaro, Inda suka baiyana cewa hukumomi sun sani sarai cewa akwai barazana, ganin yadda ake gudanar da ayyukan yan taware a Balochistan da kuma lardin Khyber Pakhtunkhwa."

Sai dai a bangaren Hukumomin Pakistan sun ce, ana kara tsaurara matakan tsaro. 
Ya yin da a garin Peshawar na lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke arewa maso yammacin kasar, 'yan sanda sun cafke wasu 'yan mutum biyu da wata mata a wani samame da suka kai a wani wurin da ake zargin dan kunar bakin wake ya boye Kafin ya kai harin.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: