Ministan harkokin wajen Iran ya ce irin hasarar rayukan Al'umma da Isra'ila ta yi a zirin Gaza ya sosa rayuwakan Al'ummar duniya

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce irin hasarar rayukan Al'umma da Isra'ila ta yi a zirin Gaza ya sosa rayuwakan Al'ummar duniya

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce irin hasarar rayukan Al'umma da Isra'ila ta yi a zirin Gaza ya sosa rayuwakan Al'ummar duniya da zuciyoyin Al'ummar musulmi.

Ya yi jawabin ne a wani taron tattaunawa da Kafar talabijin na Al Jazeera ya shirya a birnin Doha, babban birnin kasar Qatar a yau asabar, a a daidai lokacin da ake cigaba da samun takun saka tsakanin ƙasar Iran da Amurka.

Taron, wanda zai gudana daga ranar 7 zuwa 9 ga watan Fabrairu, zai yi dubi kan irin sauyin yanayin siyasar yankin gabas ta tsakiya, bisa la'akari da sakamakon yakin kisan Ƙare dangi da Isra'ila ta yi a zirin Gaza, da kuma muhimmiyar rawar da ta taka wajen sake fasalin yanayin siyasa a kasar Syria, tun daga faduwar gwamnatin Assad, da tattaunawa kan ma'aunin ikon yankin da na kasa da kasa, da kuma tasirinsu kan makomar yankin da dangantakar kasashen duniya.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: