Tattaunawar Amurka da Iran 'ya yi kyau', kuma muna sa ran karin tattaunawar anan gaba - Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka ta yi “tattaunawa mai kyau sosai” kan nukiliyan Kasar Iran bayan da bangarorin biyu suka yi wata tattaunawa ta kai tsaye a Oman, inda suka yi alkawarin sake tattaunawa a mako mai zuwa.
A nata bangaren, Iran ta ce tana sa ran gudanar da karin tattaunawa da Amurka, inda ta yaba da yanayi mai kyau a yayin tattaunawar da ake yi a yankin Gulf.
Tare da tawagar sojojin ruwan Amurka karkashin jagorancin wani jirgin ruwa a Gabas ta Tsakiya, wakilan Amurka da Iran sun gudanar da tattaunawar a birnin Muscat, babban birnin ƙasar Omsn a ranar Juma'a wanda Hukumomin Oman din suka shiga tsakani ba tare da sun gana da juna ba.
"Mu ma mun yi tattaunawa mai kyau kan Iran," ya yin da Trump ke sanar da manema labarai a cikin jirgin Air Force One a kan hanyarsa ta zuwa wurin shakatawasa na Mar-a-Lago a Florida

0 Comments:
Post a Comment