Jerin Sunayen jam'iyyu 21 da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta fitar gabanin babban zaben 2027.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa ta sanar da sunayen jam'iyyu 21 da ake da su a ƙasar nan bayan amincewa da yi wa sabbin jam’iyyun siyasa biyu rajista gabanin babban zabe na 2027.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ne ya sanar da matakin a ranar Alhamis a Abuja a taron tuntubar juna na farko da hukumar ta yi da jam’iyyun siyasa a shekarar 2026.
Amupitan ya ce hukumar ta amince da Democratic Leadership Alliance da Nigeria Democratic Congress a matsayin jam’iyyun siyasa.
Ya ce DLA ce kawai ta cika dukkan sharuddan da doka ta gindaya bayan an yi tsatsauran bincike kan jam'iyyu masu bukatar amincewa su 171 da suka nemi rajista, yayin da hukumar za ta kuma bi umarnin babbar kotun tarayya da ta bayar da umarnin yin rajistar NDC.
Biyo bayan yi wa sabbin Jam'iyyun biyu rijista hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da cewa adadin jam’iyyun siyasar kasar nan ya kai 21.
Kamar yadda aka wallafa a shafin yanar gizo na hukumar.
Ga jerin sunayen jam'iyyun a kasa.
1- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
2- Jam'iyyar PDP
3- Accord (A)
4- Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP)
5- Jam'iyyar Labor (LP)
6- All Progressives Grand Alliance (APGA)
7- African Democratic Congress (ADC)
8- Boot Party (BP)
9- Action Democratic Party (ADP)
10- African Action Congress (AAC)
11- Action Alliance (AA)
12- National Rescue Movement (NRM)
13- Zenith Labour Party (ZLP)
14- New Nigeria Peoples Party (NNPP)
15- Allied Peoples Movement (APM)
16- Peoples Redemption Party (PRP)
17- Action Peoples Party (APP)
18- Young Progressives Party (YPP)
19- Jam'iyyar Matasa (YP)
20- Democratic Leadership Alliance (DLA) - sabuwar jam'iyya.
21- Nigeria Democratic Congress (NDC) - sabuwar jam'iyya.
_1.webp)
0 Comments:
Post a Comment