Ban yi kuskure ba wajen yada bidiyon da ke nuna Barrack Obama a matsayin biri ba, - Donald Trump.

Ban yi kuskure ba wajen yada bidiyon da ke nuna Barrack Obama a matsayin biri ba, - Donald Trump.

Ban yi kuskure ba wajen yada bidiyon da ke nuna Barrack Obama a matsayin biri ba, - Donald Trump.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce bai yi kuskure ba saboda wani faifan bidiyo da aka watsa a takaice a shafinsa na Truth Social wanda ke nuna tsohon shugaban kasar Barack Obama da uwargidan tsohon shugaban kasar Michelle Obama a matsayin birai.

Da yake magana da yammacin Juma'a ga manema labarai da ke raka shi a cikin jirgin Air Force One, Trump ya dage cewa bai yi kuskure ba ta hanyar yada bidiyon kuma baya bukatar neman gafara.

"Ban yi kuskure ba," in ji shi.

Trump ya bayyana cewa bai kalli faifan gaba dayansa ba kafin a yada shi shafinsa.

Da aka tambaye shi kai tsaye ko ya yi Allah wadai da abubuwan da ke cikin bidiyon, Trump ya amsa da cewa, "Hakika na yi."

Bidiyon, wanda aka watsa shi da yammacin ranar alhamis, ya nuna wani makirci game da na'urorin zabe da aka yi amfani da su a lokacin zaben 2020 kuma ya hada da hoton wariyar launin fata na Obama da matarshi.

Kuma ya kasance akan shafin Trump na tsawon kusan awanni 12 kafin a goge shi a safiyar Juma'a, biyo bayan shan suka da Allah-wadai daga sassan ƙasar da ma duniya baki daya. 

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: