Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya halarci daurin auren ‘ya’yan karamin ministan tsaro, Bello Matawalle su tara.

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya halarci daurin auren ‘ya’yan karamin ministan tsaro, Bello Matawalle su tara.

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya halarci daurin auren ‘ya’yan karamin ministan tsaro, Bello Matawalle su tara.

Bikin wanda aka gudanar a babban masallacin kasa dake Abuja, shugaban kasar ya jagoranci wata babbar tawaga ta manyan masu fada aji a Najeriya domin karrama iyalan ministan.

Mataimakin Tinubu akan harkan sadarwa, Dada Olusegun ne ya bayyana hakan a cikin wani faifan bidiyo da aka yada a ranar Juma'a.

Taken labarin ya kara da cewa, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu a yau ya halarci daurin auren ‘ya’yan karamin ministan tsaro, wanda aka gudanar a babban masallacin kasa dake Abuja.”

Sauran manyan baki da suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Hon.Barau Jibrin da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya) da Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf da gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, da dai sauransu.

Daura auren ya kasance abin jan hankali ga jama’a tun watan Janairu, lokacin da katin gayyata na bikin ‘ya’yan Matawalle su tara ya fara bayyana.

‘Ya’yan nasa da aka aurar a wannan gagarumin aure mai dimbin tarihi sun hada da Ibrahim, Suraj, Safiya, Maryam, Aisha, Fahad, Muh’d, Nana Firdausi, da Farida.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: