Matar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kai ziyarar ban girma ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a gidansa dake kasar Saudiyya.

Matar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kai ziyarar ban girma ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar

Matar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kai ziyarar ban girma ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a gidansa dake kasar Saudiyya.

Uwargidan tsohon shugaban kasar ta samu rakiyar wasu ’yan uwa har da diyarta.

Atiku wanda ya wallafa hoton ziyarar a shafukan sada zumunta, ya ce ya ji dadin hakan.

"An karrama ni ne, na karbi bakuncin Hajiya Aisha Buhari, matar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da 'yarta Hanan da sauran 'yan uwa a ziyarar da suka kawo min a kasar Saudiyya, kamar ni, uwargidan tsohon shugaban kasa da danginta suna kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Ummarah". Inji Shi.

Atiku da Marigayi Buhari sun kasance manyan jiga-jigan siyasa wadanda fafatawarsu da juna ya haifar da yanayin siyasar Najeriya shekaru da dama, inda suka fafata da juna a zabukan shugaban kasa daban-daban. 
Duk da bambance-bambancen da ke tsakanin su na siyasa, mutanen biyu sukan fito fili suna bayyana rawar da suke ke takawa a tafiyar dimokuradiyyar Najeriya.

Kamar Atiku, itama Aisha 'yar asalin jihar Adamawa ce.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form