Wasu 'yan Senegal 18 da aka tsare a Morocco saboda rikicin da ya barke a lokac wasan karshe na gasar AFCON sun shiga yajin ƙin cin abinci.

Mintuna kadan kafin kammala wasan na watan jiya, wasu magoya bayan Senegal sun yi yunkurin kutsa kai cikin filin wasan yayin da ‘yan wasan Senegal suka dakatar da wasan na kusan mintuna 20 don nuna rashin amincewarsu da bugun fanareti da aka baiwa Morocco.

An kuma ga wasu magoya bayansu suna jefa abubuwa a filin, ciki har da kujera.

Kungiyar ta ce ana tauye musu hakkinsu na yin adalci, kuma sun yi alkawarin ci gaba da yajin aikin "har sai shari'ar Moroko ta ba mu damar a saurare mu", in ji Kabou.
Magoya bayan kwallon kafar Senegal 18 da aka tsare a Maroko saboda tayar da rikici a lokacin wasan karshe na gasar cin kofin Afrika da aka gudanar a watan jiya, sun fara yajin kin cin abinci a daidai lokacin da suke dakun shari'arsu, kamar yadda lauyansu ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Juma'a.

Lauyan Patrick Kabou ya ce wadanda yake karewa sun shaida masa cewa "tun ranar 18 ga watan Janairu suke dakon sanin tuhume-tuhumen da ake yi musu", ranar da aka kama su bayan wasan karshe na gasar AFCON da Senegal ta doke Morocco a Rabat.

Kabou ya ce kungiyar ta yi korafin cewa jami’an ‘yan sanda sun yi musu tambayoyi cikin harshen Faransanci da Larabci, yayin da “su yaren Wolof kawai suke ji”, harshensu na asali.

Mintuna kadan kafin kammala wasan na watan jiya, wasu magoya bayan Senegal sun yi yunkurin kutsa kai cikin filin wasan yayin da ‘yan wasan Senegal suka dakatar da wasan na kusan mintuna 20 don nuna rashin amincewarsu da bugun fanareti da aka baiwa Morocco.

An kuma ga wasu magoya bayansu suna jefa abubuwa a filin, ciki har da kujera.

Mutanen sun ce ana tauye musu hakkinsu na yin adalci, kuma sun yi alkawarin ci gaba da yajin kin cin abincin "har sai ma'aikatar shari'ar Moroko ta ba mu damar a saurare mu", in ji Kabou.

Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post

Contact Form