Jirgin sama dauke da fasinjoji da dama ya sauka a babban birnin ƙasar Sudan, Khartoum karon farko cikin Shekaru biyu.
Filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa da ke birnin Khartoum ya samu jirgin farko na kasuwanci da aka shirya saukar shi cikin sama da shekaru biyu yayin da gwamnatin Sudan ke ci gaba da tabbatar da ikonta a babban birnin ƙasar bayan kwashe shekaru biyu ana gwabzawa yaki.
Jirgin na Sudan Airways ya yi tattakin ne zuwa birnin Khartoum daga birnin Port Sudan da ke gabar tekun Red Sea a ranar Lahadi, dauke da fasinjoji da dama.
Da yake bayar da rahoto daga kusa da filin da jirgin ya sauka, Taher Almardi na tashar talabijin na Al Jazeera ya bayyana al'amuran murna bayan isowar jirgin.
Ya ce sake bude filin jirgin zai taimaka wajen hada babban birnin kasar da wasu yankuna na kasar Sudan, inda jami'ai suka ce a yanzu haka cibiyar a shirye take ta yi maraba da jiragen sama har guda hudu a kullum.
A cikin wata sanarwa da kamfanin jirgin Sudan Airways ya fitar, ya ce jirgin wanda aka sanar a ranar Asabar da farashin tikitinsa da ya fara daga dala 50, "yana nuna dawowar ruhi da kuma ci gaba da alaka tsakanin 'yan kasar".
_2.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment