Idan Amurka ta kaiwa wa Ƙasar Iran hari zai haifar da mummunar yaki da zai shafi yankin gabas ta tsakiya.

Idan Amurka ta kaiwa wa Ƙasar Iran hari zai haifar da mummunar yaki da zai shafi yankin gabas ta tsakiya.

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya gargadi Amurka cewa duk wani hari da za a kai wa kasarsa zai haifar da " mumunar yaki da zai shafi yankin gabas ta tsakiya".
Ya fadi haka ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke cigaba da tara jiragen yaƙin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya da nufin kaddamar da harin akan Jumhuriyar musulci ta Iran.

"Ya kamata su sani cewa idan suka fara yaki a wannan karon, to zai zama yaki ne da zai shafi yankin baki daya," in ji shugaban kolin mai shekaru 86,  a Lokacin wani taro da aka yi a birnin Tehran a yau Lahadi.

Shugaban kolin na Iran ya Kuma zargi Amurka da nufin kwace albarkatun man fetur da iskar gas na kasarsa.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: