'Yan bindiga sun kona ofishin ‘yan sanda da wani bangare na coci a jihar Neja.

'Yan bindiga sun kona ofishin ‘yan sanda da wani bangare na coci a jihar Neja.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kona ofishin ‘yan sanda da wani bangare na coci a unguwar Agwara da sanyin safiyar yau Lahadi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Minna yau Lahadi.

Abiodun ya ce an kai harin ne da misalin karfe 3:40 na asubahi, lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki ofishin ‘yan sanda na Agwara.

Ya ce rundunar ‘yan sandan da ke bakin aikin ta ne suka yi artabu da maharan, inda ya ce daga baya ‘yan bindigar sun yi galaba a kan jami’an, inda suka yi amfani da karfin tuwo wajen cinna wa ofishin wuta.

A cewarsa, "Daga baya maharan sun koma Cocin United Methodist Church (UMC) da ke unguwar, inda suka kona wani bangare na ginin cocin."

Kakakin ‘yan sandan ya kuma ce daga bisani ‘yan bindigar sun zarce zuwa wasu yankunan al’ummar inda suka yi awon gaba da mutane kusan biyar, wadanda har yanzu ba a tantance ko su waye ba.

Ya kuma bada tabbacin cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike tare da kara kaimi wajen zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika da kuma kubutar da wadanda aka sace.

Jihar Neja da ke arewa maso yammacin Najeriya na fama da yawaitar hare-haren 'yan fashi da makami daga kungiyoyin masu aikata laifuka.

Inda ko a watan Nuwambar 2025, ‘yan bindiga sai da suka sace dalibai sama da 300 da malamai 12 daga makarantar St. Mary’s da ke Papiri.

Haka Kuma a ranar 3 ga watan Janairu, wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai a kan babura sun kashe mazaje 42, sannan suka yi awon gaba da mata da kananan yara a kauyen Kasuwan Daji da ke karamar hukumar Agwara, tare da kona kasuwa da gidaje.

Wadannan al’amura sun nuna yadda ake ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro a jihar.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: