Hukumar kashe gobara ta gano gawar wani yaro dan shekara uku da ya fada rijiya ba'a sani ba a Kano

Hukumar kashe gobara ta gano gawar wani yaro dan shekara uku da ya fada rijiya ba'a sani ba a Kano

Hukumar kashe gobara ta gano gawar wani yaro dan shekara uku da ya fada rijiya ba'a sani ba a Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta gano gawar wani yaro dan shekara uku mai suna Abdura’uf Badamasi, wanda aka ce ya bace a kauyen Wangara da ke karamar hukumar Tofa a jihar.

Daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Alhaji Saminu Abdullahi ya sanyawa hannu, kuma ya saki ranar Asabar a Kano.

Ya ce, “Mun samu kiran waya daga wani Dan Asabe Rabiu a safiyar ranar Juma’a da misalin karfe 7:50 na safe, inda ya ba mu labarin bacewar Badamasi.

“Bayan samun rahoton, nan take aka tura tawagar ceto daga hedkwatar hukumar zuwa wurin.

"Da isar su, aka bayyana masu cewa Badamasi ya bata tun ranar Alhamis da yamma, inda iyayensa ke zargin cewa watakila ya fada rijiya."

Abdullahi ya bayyana cewa jami’an kashe gobara sun shiga cikin wata rijiyar nan da nan inda suka yi nasaran gano yaron wanda ya riga ya mutu.

Inda aka mika gawarsa ga Hakimin Kauyen Wangara domin yi masa jana’iza.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: