Isra'ila ta sake bude kan iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar bayan kusan shekaru biyu da rufewa.
Isra'ila ta sake bude kan iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar bayan kusan shekaru biyu, yayin da dubban Falasdinawa marasa lafiya da wadanda suka jikkata ke neman kulawar gaggawa a kasashen waje.
Bude Kan iyakar ta Rafah yazo ne kwana daya bayan harin da Israi'la ta kai zirin Gaza da Khan Younis yayi sanadin mutuwar Falasdinawa 31 ciki har da yara shida, Inda ya kasance hari mafi muni da zubar da jini tun bayan da aka kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Kungiyar Hamas da Israi'la a watan Oktoban 2025.
Sojojin Isra'ila sun kashe akalla Falasdinawa 509 tare da raunata wasu 1,405 tun bayan fara aikin yarjejeniyar "tsagaita wuta".

0 Comments:
Post a Comment