Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta sanar da kashe wasu ‘yan bindiga uku da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, tare da kwato makamai da alburusai, da kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, biyo bayan hadin gwiwa da jami’an tsaro suka gudanar a kan iyakokin jihar.
Da yake zantawa da , jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa tun da farko jami’an tsaro sun dakile wani yunkurin kai hari da ‘yan bindiga suka yi a ranar Juma’a a kusa da yankin Pindiga, Billiri, da Shongom, wadanda ke kan iyaka da jihar Adamawa.
Ya kara da cewa, "A safiyar ranar Asabar, da karfe 3 na safe, sun je Garin Galadima, Lambo, inda suka kashe daya tare da yin awon gaba da mutum biyar." Lamarin da ya janyo daukin gaggawa daga jami’an tsaro da ‘yan banga na yankin.

0 Comments:
Post a Comment