Likitoci 40,000 ne ke da lasisin aiki a Najeriya, yayin da rahoto ya baiyana bukatuwar Aƙalla likitoci 300,000 domin duba lafiyar Al'ummar ƙasar mai mutane sama da miliyan 220.
Tsarin kiwon lafiyan Najeriya wanda ya dade da yin rauni yana fuskantar karancin ma'aikata, yayin da adadin likitocin da ke da lasisi ya ragu zuwa kusan 40,000, kasa da kiyasin 300,000 da ake bukata don samar da isasshiyar hidima ga al'ummar sama da miliyan 220, kamar yadda Rahotan HealthWise na jaridar Punchng ya ruwanto.
A shekarar 2024, ministan lafiya da walwalar jama'a, Farfesa Muhammad Pate, ya bayyana cewa Najeriya na da likitoci kusan 55,000 da suka mallaki lasisin aiki.
Da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels TV’s Politics, Pate ya bayyana cewa a kalla likitoci 16,000 ne suka bar kasar a cikin shekaru biyar da suka gabata, yayin da wasu kusan 17,000 aka dauke su daga bakin aiki.
Wani abin damuwa shine, yadda wani sabon fallasa da kwamishinan lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya yi, inda ya baiyana cewa adadin likitocin da ke aiki a Najeriya ya ragu daga 55,000 zuwa 40,000 a cikin shekara guda kacal.
A jawabin da ya gabatar a wani taron tattaunawa na kwana daya da aka gudanar a Legas mai taken “Karfafa Tsarin cibiyoyin Kiwon lafiya na farko : da Tattaunawar Shugabanci na hadin gwiwa,” Abayomi ya bayyana karancin ma’aikata a matsayin daya daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar bangaren lafiya a Najeriya.

0 Comments:
Post a Comment