Babban Injin da ke samar da wutan lantarki a Najeriya ya sake samun matsala, a karo na biyu cikin kwanaki biyar.
Wutar lantarki ta kasa ta sake yin ƙasar a safiyar yau, 27 ga watan Janairu, lamarin da ya jefa wasu sassan kasar cikin duhu tare da kawo cikas ga harkokin wutar lantarki a fadin kasar.
Wannan matsalar shine karo na biyu a cikin mako guda da wutan ya samu matsala.
A halin yanzu kamfanin samar da wutar lantarki na Delta Gas Power Plant ne kawai ke samar da wutar lantarki, inda ya ke bayar da gudunmawar wutan lantarki Mai karfin megawatt 39 ga tashar.

0 Comments:
Post a Comment