Ƙasar Koriya ta Arewa ta sake yin gwajin makami mai linzamin a kan tekun ƙasar Japan karo na biyu a cikin wata daya.
Ma'aikatar tsaron Japan ta ce Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami kan tekun kasar a yau Talata.
Gwajin dai shi ne karo na biyu da Kasar ta Koriya ta Arewa ta yi a cikin wannan watan, biyo bayan harba makami mai linzami da tayi sa'o'i kadan kafin shugaban Koriya ta Kudu ya nufi ƙasar China domin gudanar da wani taro a ranar 4 ga wannan watan.
Koriya ta Arewa ta kasance tana yin gwajin makami mai linzami akai-akai a cikin 'yan shekarun nan duk da matsin lamba da takunkumin karya tattalin arziki da Kasashen yamma ke sanya mata.

0 Comments:
Post a Comment