Kotu ta yi fatali da bukatar Nnamdi Kanu na neman a sauya mashi sheka daga gidan yarin jihar Sokoto.
A safiyan yau Talata ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi fatali da bukatar da shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB) Nnamdi Kanu ya shigar na neman a dauke shi daga gidan yari na jihar Sokoto.
Kotun, a hukuncin da mai shari’a James Omotosho, ya yanke, ta ce bukatar bai dace ba.
Kanu, wanda kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai a ranar 20 ga Nuwamba, 2025, ya sanya hannu kan cewa tsare shi a gidan yari na Sakkwato zai kawo masa cikas wajen daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa.
A cikin wasu dalilai guda takwas da ya gabatar na goyon bayan kudirin mai lamba FHC/ABJ/CR/383/2015, shugaban kungiyar ta IPOB, ya bayyana cewa kotu bayan ta same shi da laifuka bakwai na ta’addanci, da gwamnati ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai a duk wani gidan gyaran hali na kasar nan in banda Kujerun Correction na Abuja.

0 Comments:
Post a Comment