Rundunar tsaron Najeriya ta fitar da jerin sunayen sojoji 16 da ake zargi da yunkurin yin juyin mulki ga Shugaban ƙasar, Bola Tinubu.
Hedikwatar tsaro (DHQ) ta fitar da cikakken jerin sunayen hafsoshi 16 na rundunar sojin Najeriya da wata hukumar bincike ta musamman ta gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin yunkurin juyin mulkin da aka shirya yi wa shugaba Bola Tinubu.
Kwamitin dai ya tuhumi sojoji 16 da aikata manyan laifuka, ciki har da yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu.
Daraktan yada labarai na rundunar tsaron, Manjo Janar Samaila Uba, ya bayyana cewa kwamitin ya kammala bincikensa inda ya gano cewa da yawa daga cikin jami’an na da karar da za su amsa.
Ya ce yanzu haka hafsoshin da ake zargi za su fuskanci Kotun Soji kamar yadda aka kafa da kuma tsara wasu ka’idoji.
Ga cikakkun sunayen da mukaman jami’an 16 da ake tuhuma a kasa:
1. Brigadier General Musa Abubakar Sadiq (Nasarawa, 44th Regular Course)
2. Colonel M. A. Ma’aji (Niger, 47th Regular Course)
3. Lieutenant Colonel S. Bappah (Bauchi, 56th Regular Course)
4. Lieutenant Colonel A. A. Hayatu (Kaduna, 56th Regular Course)
5. Lieutenant Colonel Dangnan (Plateau, 56th Regular Course)
6. Lieutenant Colonel M. Almakura (Nasarawa, 56th Regular Course)
7. Major A. J. Ibrahim (Gombe, 56th Regular Course)
8. Major M. M. Jiddah (Katsina, 56th Regular Course)
9. Major M. A. Usman (Federal Capital Territory, 60th Regular Course)
10. Major D. Yusuf (Gombe, 59th Regular Course)
11. Major I. Dauda (Jigawa, DSSC 38)
12. Captain I. Bello (DSSC 43)
13. Captain A. A. Yusuf
14. Lieutenant S. S. Felix (DSSC)
15. Lieutenant Commander D. B.
16. Abdullahi (Nigerian Navy)
Squadron Leader S. B. Adamu (Nigerian Air Force).

0 Comments:
Post a Comment