Trump ya yi gargadin ƙara kai hare-hare a Najeriya idan aka ci gaba da kashe kiristoci a ƙasar.

Trump ya yi gargadin ƙara kai hare-hare a Najeriya idan aka ci gaba da kashe kiristoci a ƙasar.

Trump ya yi gargadin ƙara kai hare-hare a Najeriya idan aka ci gaba da kashe kiristoci a ƙasar.

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar New York Times da aka buga a ranar Alhamis, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna cewa Amurka za ta iya kai hare-hare da dama a Najeriya idan aka ci gaba da cin zarafin Kiristoci.

Trump, wanda aka tambaye shi ko harin da sojoji suka kai kan mayakan IS a arewa maso yammacin Najeriya a ranar 25 ga watan Disamba, ya nuna fara wani gagarumin yakar su ne, sai ya ce, “Zan so in sake Kai hari daya ne kawai, amma idan suka ci gaba da kashe Kiristoci, zai zama mai yawa.

Harin na Amurka, wanda Washington ta bayyana da cewa ya shafi kungiyoyin IS ne bisa bukatar gwamnatin Najeriya, ya ja hankalin duniya a lokacin da aka kai harin a ranar Kirsimeti.

Trump ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martani ga abin da ya bayyana a matsayin maimaita kashe-kashen da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi suke yi wa kiristoci a Najeriya, lamarin da ya haifar da cece-kuce kan musabbabin shiga tsakani.



SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: