Akalla Falasdinawa uku ne suka mutu yayin a sabbin hare-haren da Israi'la ta kai Gaza

Akalla Falasdinawa uku ne suka mutu yayin a sabbin hare-haren da Israi'la ta kai Gaza

Akalla Falasdinawa uku ne suka mutu yayin da 7 suka jikkata a sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai cikin dare a Gaza, wanda hakan ya sabawa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a watan Oktoba tsakanin Isra'ila da Hamas.

Falasdinawa uku ne suka mutu sannan bakwai suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a yankuna daban-daban na zirin Gaza a ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakaninta da Kungiyar Hamas a cewar majiyoyin lafiya dake Gaza.

Majiyoyi sun shaida wa Al Jazeera yankunan da Isra'ila ta kai farmaki cikin dare zuwa ranar Lahadi sun hada da Rafah da Khan Younis a kudancin Gaza, da unguwar Zeitoun da ke kudu maso gabashin birnin Gaza da kuma wasu yankuna daban-daban a fadin yankin da aka yi wa kawanya, yayin da hare-haren kisan kare dangi da Isra'ila ke ci gaba akan Al'ummar Falastinawa.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: