Sama da mutane 200 ne suka mutu sakamakon ruftawar mahakar ma'adinai a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
Sama da mutane 200 ne rahotanni suka ce sun mutu sakamakon ruftawar mahakar ma'adinan Rubaya coltan da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo.
Lumumba Kambere Muyisa, kakakin gwamnan lardin wanda 'yan tawaye suka nada a lardin da mahakar ta ke, shine ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa mahakar ma'adinan mai tazarar kilomita 60 daga arewa maso yammacin birnin Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa ta ruguje ne a ranar Larabar da ta gabata, kuma har yanzu ba a san takamaiman adadin wadanda suka mutu ba.
Kungiyoyin kare hakkin sun nuna damuwa game da yanayin mahakar ma'adinan, wacce ke samar da kusan kashi 15 cikin 100 na ma'adanin coltan na duniya da ake amfani da shi a wajen hada na'urorin lantarki na zamani.

0 Comments:
Post a Comment