Iran ta sanar da yin atisayen soji a mashigar ruwan Hormuz kusa da jiragen ruwan yakin Amurka yayin da ake cigaba da zaman dar-dar a yankin.
Iran ta sanar da wani atisayen kwana biyu a mashigar ruwan Hormuz, wanda zai fara a ranar Lahadi, bayan da Amurka ta tura jirgin Abraham Lincoln da wasu manyan jiragen yakin sojin ta zuwa yankin gabas ta tsakiya.
Sai dai babban kwamandan rundunar sojin Amurka ta (CENTCOM) ya yi gargadi ga sojojin kasar Iran, yana mai cewa ba za su lamunta da shawagin jiragen sama a kan jiragen yakin Amurka ba, ciki har da kaiwa da komowan jiragen ruwan Iran da ke atisayen tsaro a kusa da jiragen ruwan Amurka.
An shafe makonni ana takun saka tsakanin Iran da Amurka a daidai lokacin da Trump ya sha yin barazanar kai wa Iran hari saboda murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnati da kuma yunkurinsa na dakile shirin nukiliyar Iran.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi a ranar Juma'a ya ce kasarsa a shirye take don yin tattaunawa "daidai da adalci", amma ba zata amince da bukatar Trump na tsakiya ba.
Dabarun tsaro da tsarin makami mai linzami ba zai taba zama batun tattaunawar ba, in ji Araghchi.
_5.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment