Akalla Falasdinawa 12, rabinsu kananan yara ne aka kashe a zirin Gaza, kwana guda kafin a sake bude mashigar Rafah.

Akalla Falasdinawa 12, rabinsu kananan yara ne aka kashe a zirin Gaza, kwana guda kafin a sake bude mashigar Rafah.

Akalla Falasdinawa 12, rabinsu kananan yara ne aka kashe a zirin Gaza, kwana guda kafin a sake bude mashigar Rafah.

Wani hari ta sama da Isra’ila ta kai a ranar Asabar a wani tanti da ke matsugunin ‘yan gudun hijira a yankin al-Mawasi da ke arewa maso yammacin birnin Khan Younis, ya kashe Falasdinawa akalla bakwai, ciki har da yara uku, kamar yadda majiyoyin lafiya suka shaida wa tashar talabijin na Al Jazeera.

An kai gawarwakinsu zuwa cibiyar kula da lafiya ta Nasser da ke Khan Younis.

A birnin Gaza, hukumar bada agajin gaggawa ta bayar da rahoton cewa, akalla Falasdinawa 5 da suka hada da kananan yara uku ne suka mutu a wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wani ginin da ke unguwar Remal da ke yammacin birnin.

Falasdinawa 8 ne kuma suka jikkata sakamakon wani harin bam da Isra'ila ta kai kan wani gini da ke unguwar Daraj a birnin Gaza.

Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya ce akalla Falasdinawan 524 ne sojojin Isra'ila suka kashe tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Amurka ta kulla a tsakanin Kungiyar Hamas da Israi'la a ta fara aiki a ranar 10 ga watan Oktoban 2025.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: