Kotu ta ba tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello izinin tafiya zuwa Ƙasa mai tsarki domin yin aikin Ummarah.
A ranar Alhamis ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta amince da bukatar da tsohon gwamna Yahaya Bello na Kogi ya yi na tafiya birnin Makkah na kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Ummarah a kwanaki 10 na karshen watan Ramadan a kasa mai tsarki.
Mai shari’a Emeka Nwite ya amince da bukatar ne bayan lauyan tsohon gwamnan, Joseph Daudu, SAN, ya gabatar da bukatar a kan haka.
Babban Lauyan ya bayyana cewa, bukatar ta nemi a ba da umarni da kuma ba da izinin sakin Fasfo na kasa da kasa na wucin gadi don ba shi damar zuwa Saudiyya don yin aikin Ummarah a watan Ramadan na bana, wanda zai fara a ranar 18 ga watan Fabrairu kuma ya kare a ranar 19 ga Maris.
Kemi Pinheiro, SAN, wacce ta bayyana a matsayin lauyar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, ba ta ki amincewa da bukatar ba.
Tun da farko a lokacin da kotu ta ba tsohon gwamnan damar bayyana kwanaki nawa yake da niyyar yi a kasar waje, ya ce duk da ya so ya yi kwanaki 30 a kasa mai tsarki, amma ya tuna da shari’ar da EFCC ke yi masa.
Bello ya ce, duk da cewa shekaru takwas da suka gabata bai yi tafiya a wajen Najeriya ba, amma zai yi kwanaki 10 na karshen watan Ramadan a Makka don yin addu’a ga Allah.

0 Comments:
Post a Comment