Kungiyar ISIL ta dauki alhakin harin da aka kai a sansanin sojojin sama a babban filin jirgin saman Nijar.
Ikirarin na zuwa ne bayan shugaban mulkin sojan Nijar, Abdourahamane Tiani ya zargi Faransa, Benin, Ivory Coast da hannu a harin.
Kamfanin dillancin labarai na Amaq mai alaka da ISIL ne ya bayar da rahoton a yau Juma'a, Inda ya baiyana cewa, kungiyar ta kai wani hari na ban mamaki da hadin gwiwa a sansanin sojin ƙasar da ke filin jirgin saman Diori Hamani da ke kusa da babban birnin kasar Yamai.
Ta yi ikirarin cewa harin ya haifar da "barna sosai", ba tare da bayar da Cikakken bayani ba.
Sai dai gwamnatin mulkin sojin Nijar din, wacce ta karbi mulki a juyin mulkin shekarar 2023, ta ce jami’an tsaron ƙasar sun kashe maharan 20 a Lokacin fadan na daren ranar Alhamis, yayin da Sojojin sojoji ta hudu suka jikkata.
_4.jpeg)
0 Comments:
Post a Comment