Adadin wadanda suka rasu a hatsarin jirgin ƙasa a Sifaniya yakai mutum 46 bayan wani fasinja ya rasu a asibiti.
Wani fasinja da ya ji rauni a hatsarin jirgin ƙasa mai gudun gaske a wannan watan a ƙasar Sifaniya ya mutu a asibiti a yau Juma'a, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane zuwa 46, in ji hukumomin kiwon lafiya na yankin.
Hatsarin na ranar 18 ga watan Janairu a kudancin Andalusia ya kasance daya daga cikin hadura mafi muni a Turai a wannan karnin, wanda hakan ya sanya shakku kan amincin tafiyar jirgin ƙasa a Sifaniya, wacce ke da babbar hanyar sufurin jirgin ƙasa mafi sauri ta biyu a duniya bayan ƙasar Sin.
Mai magana da yawun ma'aikatar lafiya ta yankin Andalusia ta shaida wa tashar AFP cewa "daya daga cikin wadanda abin ya shafa da ke kwance a asibiti ya mutu" a asibitin Reina Sofia na birnin Cordoba.
Sai dai ta kara da cewa ba a ba sashen izinin ba da wani karin bayani ba game da lamarin ba.

0 Comments:
Post a Comment