An daura auren biyu daga cikin ‘ya’yan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a Abuja

An daura auren biyu daga cikin ‘ya’yan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a Abuja

An daura auren biyu daga cikin ‘ya’yan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a babban masallacin kasa da ke Abuja.

An daura auren biyu daga cikin ‘ya’yan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a ranar Juma’a a babban masallacin kasa da ke Abuja, a wani biki da ya hada ‘yan uwa da abokan arziki da kuma manyan baki.

A wata sanarwa da ya fitar bayan taron a shafinsa na X a ranar Juma’a, Atiku ya ce bikin ya ba shi “babban farin ciki” tare da nuna godiya ga duk wadanda suka halarci bikin da kuma goyon bayan bikin.

Janar Aliyu Gusau ne ya zama waliyin diyar Atiku, Hafsat Atiku wacce aka daura mata aure da Umar Farouk Imam.

Shi ma dansa Abubakar Atiku Jr, ya  auri Asma’u Abdul’aziz Nyako, wanda Alhaji Kwairanga Jada, wani aboki Kuma makusancin Atikun ya daura masu auren.

SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: