Gwamnatin Afrika ta kudu ta sanar da korar wakilin Isra'ila a ƙasar bisa zargin cin zarafin Shugaban ƙasar a shafukan sada zumunta.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu ta sanar da korar wakilin Isra'ila a kasar, inda ta zargi jami'in na Isra'ila da yin "cin zarafin ka'idojin diflomasiyya da ba za a amince da shi ba" wanda ke kalubalantar ikon Afirka ta Kudu.
Ma'aikatar hulda da kasashen waje da hadin gwiwar kasa da kasa ta fada a ranar Juma'a cewa tana baiwa Ariel Seidman, jami'in ofishin jakadancin Isra'ila wa'adin sa'o'i 72 ya bar Afirka ta Kudu bayan da ta ayyana shi a matsayin mutumin da ba'a maraba da shi.
Ta zargi Seidman da kalamai na batanci ga shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a shafukan sada zumunta da kuma kin sanar ziyarar wasu manyan jami'an Isra'ila ƙasar da gangar".
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce "Irin wadannan ayyuka suna wakiltar babban cin zarafin diflomasiyya da kuma keta yarjejeniyar Vienna.
"Muna kira ga gwamnatin Isra'ila da ta tabbatar da ayyukan diflomasiyyarta a nan gaba da nuna girmamawa ga Jamhuriyar da ka'idojin huldar kasa da kasa."

0 Comments:
Post a Comment