Real Madrid ta sallami Kociyanta, Xabi Alonso bayan Barcelona ta doke ta a wasan karshe na cin kofin Super Cup.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kasar Sipaniya ta kori kocinta Xabi Alonso sa’o’i bayan ta sha kashi a hannun Barcelona da ci 3-2 a wasan karshe na gasar cin kofin Super Cup a birnin Jeddah na kasar Saudiyya ranar Lahadi.
Kungiyar ce ta bayyana hakan a shafinta na X a yau Litinin.
Ta rubuta, "Real Madrid ta sanar da cewa, bisa yarjejeniya tsakanin kungiyar da Xabi Alonso, an yanke shawarar kawo karshen zamansa a matsayin kociyan kungiyar.
"Xabi Alonso zai kasance yana samun kauna da sha'awar duk magoya bayan Madrid saboda shi gwarzon Real Madrid ne kuma
yana wakiltar kimar Kungiyar, a ko yaushe, Real Madrid za ta kasance gidan sa."
Kungiyar ta sanar da maye gurbin Xabi Alonson da tsohon dan wasan bayanta, Alvaro Arbeloa, wanda ke kula da karamar Kungiyar Real Madrid.

0 Comments:
Post a Comment