Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba wa masu zanga-zangar nuna goyon bayansu ga Gwamnantin ƙasar

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba wa masu zanga-zangar nuna goyon bayansu ga Gwamnantin ƙasar

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba wa masu zanga-zangar nuna goyon bayansu ga Gwamnantin ƙasar, yana mai cewa sun yi wani gagarumin aiki da ya dace, duk da cewa masu zanga-zangar kin jinin Gwamnatin na ci gaba da yin kira da a kawo karshen gwamnatin Musuluncin wacce ta shafe kusan shekaru 50 tana mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. 

Dubun dubatan Iraniyawa ne suka fito domin jaddada goyon bayansu ga Gwamnantin ƙasar da Kuma yin Allah wadai da masu zanga-zangar nunan kin jinin Gwamnatin ƙasar Saboda tsadar rayuwa da matsalar tattalin arzikin Kasar ya haifar.

Haka zalika Iran ta kira jakadunta dake Kasashen Jamus da Faransa da Italiya da Birtaniya domin tattaunawa kan abin da ta ce goyon bayan da Kasashen ke yi ga masu zanga-zangar da ake yi a fadin kasar.

An fara gudanar da zanga-zangar ne a karshen watan Disamba kan korafe-korafen tattalin arziki, amma tun daga lokacin aka koma wani salo - inda masu zanga-zangar ke neman kawo karshen Gwamnatin Jamhuriyar Musulunci da aka kafa kusan shekaru 50 da suka gabata.

An nuna wa jami’an diflomasiyyar faifan bidiyon barnar da ‘yan tarzoman suka yi, kuma sun shaida wa gwamnatocinsu cewa su “su janye kalamansu na goyon masu zanga-zangar a hukumance,” in ji ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, a cikin wata sanarwa da gidan talabijin din kasar ya fitar.


SHARE THIS

Author:

I am a blogger by passion and a Website developer by profession, I am currently the CEO of Hausalive.com.ng, a website that brings you a daily needful and useful contents.

0 Comments: