Amurka ta kai wa Najeriya muhimman kayyakin soji a ci gaba da kokarin karfafa hadin gwiwa a fannin tsaro a tsakanin kasashen biyu.
Rundunar sojin Amurka ta AFRICOM ce ta tabbatar da isar da sakon, wanda ke da alhakin ayyukan sojojin Amurka a nahiyar Afrika.
"Wannan isar da sako na goyon bayan ayyukan da Najeriya ke ci gaba da yi kuma yana jaddada kawancen tsaro na hadin gwiwa," in ji AFRICOM.
Sakon wanda aka yiwa lakabi da Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, bai bayyana takamaiman yanayi ko adadin kayan aikin sojan da aka kawo ba.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka ke Kara karfafa.
A daren kirsimeti, sojojin Amurka suka kai farmaki ta sama a jihar Sokoto, inda suka harba makami mai linzami kan mayakan da ke da alaka da kungiyar IS da ake zargi da hada kai da kungiyar jihadi ta Lakurawa da kuma kungiyoyin ‘yan bindiga na cikin gida.

0 Comments:
Post a Comment