Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da likitocin da suka manta almakashi a cikin mara lafiya, wanda yayi sanadin rasa ranta.
Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta dakatar da wasu ma’aikatan jinya uku a cibiyar Abubakar Imam Urology Center bayan da aka manta da wani almakashin fida a cikin wata mara lafiya, Aishatu Umar mai ‘ya’ya biyar, wanda ya kai ga rasuwarta a ranar 11 ga watan Junairu, 2026.
Aishatu dai ta je asibiti ne domin duba lafiyarsa a watan Satumbar 2025, sai dai bayan an yi mata aikin, sai ta ji bata jin dadi, hakan yasa aka yi mata gwaje-gwaje da hoto, inda aka gano cewa akwai almakashi a cikinta.
Lamarin dai ya haifar da cece-kuce kan yadda gwamnati za ta hukunta likitan.
Da take mayar da martani kan koke-koke da jama’a suka yi, hukumar gudanarwar asibitocin jihar a wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na asibitin, Samira Suleiman, ta ce binciken farko da babban sakataren gudanarwa, Dokta Mansur Mudi Nagoda ya bayar, ya tabbatar da cewa an bar almakashi na fida a jikin majinyacin bayan an yi masa aiki.
Hukumar ta sanar da dakatar da wasu ma’aikata uku da ke da hannu kai tsaye daga aikin jinya.
Haka kuma ta mika lamarin ga kwamitin da’ar likitoci ta jihar Kano domin ci gaba da bincike da kuma daukar matakan ladabtarwa bisa ka’idojin kwararru da kuma doka.
Sanarwar ta kara da cewa "Hukumar tana mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiya Aishatu Umar tare da jajanta musu kan wannan rashi mai raɗaɗi, muna tabbatar wa jama'a cewa ba za a lamunci sakaci ta kowace hanya ba," in ji sanarwar.

0 Comments:
Post a Comment