Sama da mutane 10 ne suka mutu ciki har da kansila mai ci bayan wani sabon rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Donga ta jihar Taraba.
Daga cikin wadanda aka kashe har da kansila .
Wata majiya a garin Donga Lawal Adamu ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa rikicin ya barke ne a ranar Asabar a kauyen Gundom.
Ya ce an samu matsala ne a lokacin da wani makiyayi ya kai shanunsa wata gona a kauyen, inda suka lalata amfanin gonan.
A cewarsa, mutanen kauyen sun kama makiyayin tare da kashe shi, lamarin da ya haifar da tashin hankali tsakanin manoman da makiyaya a yankin.
Lawal ya ce rikicin da ya biyo baya yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da goma ciki har da kansila mai wakiltar gundumar Akete a karamar hukumar Donga .
Ya kara da cewa ba za a iya tantance hakikanin adadin wadanda suka mutu daga bangarorin biyu ba har ya zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, ASP Victor Mshelizah, ya tabbatar da faruwar lamarin.

0 Comments:
Post a Comment