Wasu fusatattun matasa sun fatattaki ‘yan kasuwar Hausawa a kasuwar dabbobi da ke Ekpoma a Edo ta tsakiya inda suka rinka yanka dabbobi tare da fatattakan ‘yan kasuwar daga wajen sana'ar ta su.
A ranar Asabar ne mazauna yankin suka yi zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu da kisan da aka yi wa wani matashi a hannun wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a yankin.
Wanda hakan ne yasa suka fantsama cikin kasuwar dabbobi domin ɗaukar fansa akan Al'ummar hausawa dake gudanar da sana'arsu a wajen.
A faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo a safiyar yau Lahadi, an nuna yadda matasan suka shiga kasuwar dabbobin, inda suka rinka yanka awaki tare da fatattakar ‘yan kasuwar.
Kwamishinan Yada Labarai da Dabaru na Jihar Edo, Kassim Afegbua, ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da yin kira da a kwantar da hankula domin kaucewa harin ramuwar gayya a wasu wurare.
Ya ce tuni Gwamna Monday Okpebolo ya isa Ekpoma domin yin kira da a kwantar da hankula, yana mai bayyana hakan a matsayin wani yunkuri na gungun mutane da bai dace ba.
Ya ce, “Wannan abu ne da ba za a iya mantawa da shi ba, ba zato ba tsammani, muna rokon a kwantar da hankula, don guje wa harin ramuwar gayya a wasu wurare.
"Gwamnan ya je yankin ne domin neman a kwantar da hankula, inda yace daukar doka a hannu ba shine mafi kyawun hanya ba."

0 Comments:
Post a Comment